Vermaelen ya sabunta kwangilarsa a Arsenal

Thomas Vermaelen
Image caption Thomas Vermaelen

Dan kwallon bayan Arsenal Thomas Vermaelen ya kulla sabuwar yarjejeniya da kulob din don shafe lokaci mai tsawo tare da ita.

Dan wasan mai shekaru 25 wanda yake jinyar rauni a idon sawunsa, yana gabda komawa taka leda.

Vermaelen dan kasar Belgium ya koma Arsenal ne daga Ajax a watan Yunin 2009.

Vermaelen yace"Tun dama ina da niyyar cigaba da kasancewa anan".

Kafin a fara kakar wasa ta bana ne dai Arsenal ta rasa Cesc Fabregas zuwa Barcelona da kuma Samir Nasri zuwa Manchester City.

Haka zalika ana hasashen cewar watakila kyaftin Robin van Persie zai bar Emirates saboda yaki amincewa ya sabunta kwangilarsa.

Kwangilar Van Persie zata kare ne a shekara ta 2013.