'Yan Liverpool na tare da Suarez-Dalglish

suearez da evra Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Suarez da Evra

Kocin Liverpool Kenny Dalglish ya ce kulob din na goyon bayan Luis Suarez dari bisa dari bayanda Patrice Evra ya zargesa dayin kalaman wariyar launin fata.

Evra na Manchester United ya ce Suarez ya gaya mashi kalaman batanci a wasa tsakanin United da Liverpool a ranar Asabar data wuce.

Dalglish yace"Kowa a kulob din na tare dashi a aikace da kuma bayyanne".

A farkon wannan makonne Suarez ya karyata zargin inda yace abin ya bashi mamaki.

Amma kuma Ferguson ya ce Evra nason yabi hakkinsa akan zargin.

Hukumar kwallon Ingila FA na binciken zargin.

Shugaban kungiyar 'yan kwallo a Ingila wato PFA Gordon Taylor na shirin sasanta tsakanin Suarez da Evra.