Sai na samu tabbas sannan zan sabunta kwangilata

kalou
Image caption Salomon Kalou

Dan kwallon Ivory Coast Salomon Kalou ya bayyanawa Chelsea cewar sai an tabbatar masa zai dinga murza leda sosai kafin ya sabunta kwangilarsa a Stamford Bridge.

Kalou mai shekaru 26 na shirin barin kulob din idan kwangilarsa ta kare a karshen kakar wasa ta bana.

Amma dai kocinsa Andre Villas-Boas ya bayyana a makon daya gabata cewar sun soma tattaunawa da dan wasan akan batun sabunta kwangila.

Dole ne sai sun kamalla sasantawa tsakaninsu daga nan zuwa watan Junairu, idan ba haka ba Chelsea zata yi hasara.

Kalou ya zira kwallo daya a wasanda Chelsea ta lallasa Genk daci biyar da nema a gasar zakarun Turai.

A baya bayanan, ba a cika saka Kalou ba a wasanni Chelsea.