De Jong da Nani suna da kwarin gwiwa

dejong da nani
Image caption Nani da Nigel de Jong

Nigel de Jong ya ce Manchester City na shirin samun nasara a ranar Lahadi a wasa tsakaninta da United don cigaba da kasancewa a saman teburin gasar Premier.

Amma zasu kara ne da Manchester United wacce keda kwarin gwiwa kamar yadda Nani yace.

United ta samu nasara a wasanni 24 cikin 25 data buga a Old Trafford a gasar Premier, amma kuma City na kan gaba da maki biyu akan tebur.

De Jong yace"Zamu je can a matsayin na farko kuma bukatarmu itace mu cigaba da kasancewa a haka".

Nani wanda ya zira kwallaye biyu a wasan Community Sheild ta United ta doke City yace sune zasu samu nasara a karawar.

Yace"City nada zaratan 'yan wasa amma kuma da kamar wuya a doke mu a filin Old Trafford".