Chelsea na kan hanyar nasarori -Villa-Boas

boas Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Andre Villas-Boas

Kocin Chelsea Andre Villas-Boas ya ce kulob din na kan hanyarsa ta samun nasarori a kakar wasa ta bana.

A ranar Talata ne, Villas-Boas ya ce"Ba zai 'yafewa kansa ba' idan bai lashe kofina ba a Stamford Bridge".

Sakamakon nasarar da Chelsea ta samu akan Genk daci biyar da nema, Villas-Boas yace"A halin yanzu muna kan tafarkin daya dace na cimma burinmu".

Wannan ce babbar nasarar da Chelsea ta taba samu a gasar Zakarun Turai wato zira kwallaye biyar a raga, inda Raul Meireles, Branislav Ivanovic, Salomon Kalou da kuma kwallaye biyun da Fernando Torres ya zira.

Chelsea ta lashe kofina mafi yawa tun lokacin da Roman Abramovich ya sayi kulob din, fiye da shekaru 106 da aka kafata.