Ina son in jagoranci kulob a Ingila-Ancelotti

ancelotti
Image caption Carlo Ancelotti

Tsohon Chelsea Carlo Ancelotti ya ce yanason ya zauna a Ingila don ya jagoranci wani kulob a gasar Premier.

Chelsea ta kori dan kasar Italiyar ne a karshen kakar wasan 2011, duk da cewar a 2010 ya lashe kofina biyu.

Ancelotti ya shaidawa BBC cewar"Idan na samu dama a wani kulob a nan, zan so in zauna a Ingila ina son kasar da 'yan wasanta".

Ya kara da cewar "gasar Premier ce tafi kowacce a Turai".

A kakar wasan data wuce, Chelsea ta karke ne a matsayin ta biyu inda Manchester United ta lashe gasar, sannan kuma Chelsea din an cire ta a gasar zakarun Turai, dana FA dana Carling.

Tsohon kocin AC Milan da Juventus din ya ce baida matsala da mai kulob din Roman Abramovich.

Manajoji a Chelsea tun lokacin da Abramovich ya sayi kulob din a 2003.

* Sept 2000-June 2004 Claudio Ranieri * June 2004-Sept 2007 Jose Mourinho * Sept 2007-May 2008 Avram Grant * July 2008- Feb 2009 Luiz Felipe Scolari * Feb 2009-June 2009 Guus Hiddink * July 2009-May 2011 Carlo Ancelotti * June 2011-Present Andre Villas-Boas