Bonetti ya kai karar Zambia zuwa FIFA

bonetti
Image caption Dario Bonetti

Dario Bonetti ya ce a ranar Litinin zai kai hukumar kwallon kasar Zambia(Faz) kara zuwa Fifa.

A cewar Bonetti hukumar ta FAZ ta sama ka'ida a yarjejeniyarsa da ita.

A kori Bonetti sa'o'i 48 bayanda ya tsallakar da Zambia zuwa gasar cin kofin kwallon kasashen Afrika da za ayi a badi.

A cewarsa FAZ bata bashi bayani akan korarsa ba duk da cewar sai a watan Yulin 2012 kwangilarsa zata kare.

Shugaban Faz Kalusha Bwalya shina ya bayyanawa BBC cewar an aikewa da Bonetti takardar sallama.

Amma kuma yaki yin karin bayani akan batun.

A cewarsa zasu maida hankali akan sabon kocinsu Herve Renard.