2012: Kamaru ta doke Najeriya a fenariti

cameroun
Image caption Matan Kamaru ne zakarun Afrika

Kamaru ta samu gurbin buga gasar kwallon mata a Olympics na badi bayan ta samu galaba akan Najeriya.

A bugu na biyu da suka yi a Younde, Kamaru ta samu galaba akan Najeriya biyu da daya, abinda ya maida kididdiga uku da uku.

A bugun fenariti sai Kamaru ta doke Najeriya daci hudu da uku.

Afrika ce a watan daya gabata ta samu daya gurbin Afrika bayan ta samu galaba akan Ethiopia daci hudu da daya.