Manchester City ta lallasa United daci shida

Mario Balotelli
Image caption Mario Balotelli

Manchester City ta lallasa abokiyar hammayarta Manchester United daci shida da daya don cigaba da kasancewa akan teburin gasar Premier ta Ingila.

Mario Balotelli ya zira kwallaye biyu kafin alkalin wasa ya kori dan United Jonny Evans saboda rike dan kwallon Italiyar.

Sergio Aguero ne yaci kwallo na uku kafin Darren Fletcher ya farkewa United kwallo daya.

Edin Dzeko ya ci kwallaye biyu sannan David Silva shima ya zira kwallo daya, abinda ya baiwa City nasara a filin Old Trafford daci shida da daya.

Sakamakon wasu daga cikin wasannin Premier:

*Arsenal 3 - 1 Stoke City *Fulham 1 - 3 Everton *Wolvers 2 - 2 Swansea City *Aston Villa 1 - 2 West Bromwich Albion *Bolton Wanderers 0 - 2 Sunderland *Newcastle United 1 - 0 Wigan Athletic *Liverpool 1 - 1 Norwich City