MotoGP:Dan Italiya Simoncelli ya mutu a tsere

Simoncelli
Image caption Marco Simoncelli

Dan tseren Italiya Marco Simoncelli ya mutu sakamakon mumunar hatsarin da aka yi a tseren babur na Malaysian MotoGP a Sepang.

An dakatar da tserenne bayan zagaye biyu, lokacin da babur din Simoncelli ta fadi ta kuma wulwula sau goma sha daya sai hullar kwanonsa ta fadi.

Nan take sai Colin Edwards da Valentino Rossi wadanda suma suke kan babur suka haye kan Simoncelli.

Simoncelli ko shurawa bai yiba lokacin da lamarin ya auku, a yayinda dan Amurka Edwards yayi targade a kafada.