Wasan City shi ne mafi muni a rayuwata - Ferguson

Alex Ferguson Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Manchester City ta lallasa United da ci 6-1 a wasan

Kocin Manchester United Sir Alex Ferguson ya bayyana kashin da suka sha a hannun Manchester City da ci 6-1, da cewa shi ne "mafi muni" da ya taba gani a kulob din.

Sai dai ya ce "za su mayar da martani".

Mario Balotelli da Edin Dzeko sun zira kwallaye biyu-biyu a wasan da City ta lallasa United - inda kuma aka baiwa Jonny Evans jan kati.

Ferguson ya ce: "Shi ne wasa mafi muni da na taba fuskanta a tarihi na. Tasirin zai bayyana ne ta fuskar abin kunyar da sakamakon zai haifar."

Sergio Aguero da David Silva sun zira kwallo dai-dai a wasan da shi ne kashi mafi girma da United ta sha a filin wasa na Old Trafford tun shekarar 1955.

Ferguson ya amince cewa rashin nasarar - wanda ya kawo karshen wasanni 19 da suka shafe a jere suna samun nasara a gida - sakacinsu ne.

"Sakamakon ya yi muni amma mu muka kashe kanmu," a cewar kocin na United.

"Korar da aka yi wa Jonny Evans ta yi mana illa sosai. Da mutane 10 mun ci gaba da kai hari - wasa ne mai kyau amma muka kare shi cikin mummunan yanayi. Sai dai kawai mu ce 'mun gamu da ranarmu'.

Karin bayani