Gabon ta kusan kamalla shirya gasar 2012

gabon
Image caption Filin wasa na Libreville a Gabon

Mahukunta kwallon kafa a Gabon sun ce kasar ta shirya daukar bakuncin gasar cin kofin kasashen Afrika a watan Junairun 2012.

Sauran kasada watanni uku ayi gasar sannan a karshen wannan makonne za a rarraba yadda kasashe zasu fafata a lokacin gasar.

Har yanzu ba a kamalla ayyuka ba a filayen wasa biyu a kasar.

Kakakin kwamitin shirya gasar a Gabon Louis-Claude Moundzieoud ya shaidawa BBC cewar "muna kan lokaci kuma zuwa karshen Oktoba za a kamalla duka ayyukan".

Gabon zata dauki bakuncin gasar ce tare da Equitorial Guinea.

An gina sabon filin wasa a babban birnin kasar wato Libreville da kuma daya a birnin Franceville dake kudancin kasar.

A wata mai zuwa ne za a buga filin wasa na Libreville inda Gabon zata buga wasan sada zumunci da Brazil.