Hernandez ya sabunta kwangilarsa zuwa 2016

hernandez
Image caption Javier Hernandez

Dan kwallon Manchester United Javier Hernandez ya sabunta kwangilarsa ta karin shekaru biyar don cigaba da taka leda a Old Trafford har zuwa 2016.

Dan kasar Mexico mai shekaru 23 ya koma United ne daga Chivas de Guadalajara a watan Yulin 2010 inda ya zira kwallaye 23 a kakar wasa ta farko a kulob din.

Kocin United Sir Alex Ferguson yace "Dan wasa na karshen da ya taka muhummiyar rawa shine Ole Gunnar Solskjaer. Javier na tunamin da Ole."

Hernandez yace:"bugawa Manchester United kwallo burina ya cika."

Ya kara da cewar "ban taba tunanin cewar zan haskaka a shekara ta ta farko ba, amma nayi murnar tabbatar da makomata a United".