Najeriya ta raba gari da kocin Super Falcons

uche Hakkin mallakar hoto b
Image caption Kocin Super Falcons Eucharia Uche

Hukumar dake kula da kwallon kafa a Najeriya wato NFF ta sanarda cewar ba zata sabunta kwangilarta da kocin Super Falcons Eucharia Uche.

An kore ta ne bayan da Najeriya ta kasa samun gurbin zuwa gasar kwallon mata na Olympics a 2012.

Kakakin NFF Ademola Olajire yace" kwangilarta ta kare, babu sabuntawa".

Sai dai wata tsohuwar 'yar kwallon Najeriya Mercy Akide ta ce tana da sha'awar jagorancin Super Falcons.

Duk da cewar Eucharia ta jagoranci Najeriya lashe gasar kwallon matan Afrika, amma kuma sai Eucharia ta kasa tsallakar da kasar zuwa gasa har sau biyu.

Kasawar Najeriya samun gurbin zuwa gasar kwallon wasanni Afrika a 2011 da kuma na Olympics a 2012.

A watan Nuwambar 2010 Eucharia Uche ta jagoranci Super Falcons lashe gasar kwallon matan Afrika a karo na shida.