A sasanta akan zargin da ake yiwa Terry

boas Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Andre Villas-Boas

Kocin Chelsea Andre Villas-Boas ya goyi bayan John Terry akan zargin cewar ya yiwa dan wasan QPR Anton Ferdinand kalamai na wariyar launin fata, inda yace maganar ta wuce.

Dan kwallon Ingilan mai shekaru talatin wanda ya karyata zargin, yana jiran sakamakon binciken 'yan sanda.

Villas-Boas yace"Muna goyon bayan John, kuma yayi magana da Anton bayan wasan".

An yita rarraba hotunan bidiyo dake nuna cewar dan kwallon Chelsea yanata zagin Ferdinand.

Ferdinand baice komai ba akan batun a yayinda ake jiran binciken 'yan sanda bayan da jama'a suka yita korafi."

Villas-Boas ya kara da cewar "kulob din biyu sun gana da juna kuma maganar ta wuce".