FA na tuhumar Chelsea akan 'yan kwallonta

abramovic Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Roman Abramovic

Hukumar kwallon Ingila FA na tuhumar Chelsea akan kasa ladabtarda 'yan wasanta a karawarsu da QPR, sannan ta bukaci kocin Kulob din Andre Villas-Boas yayi karin bayani akan alkalin wasa Chris Foy.

Villas-Boas ya ce Foy ya taka mummunar rawar data yi tasiri ga makomar wasan, inda aka kori 'yan Chelsea biyu da kuma baiwa takwas katin gargadi.

A ranar Laraba ne FA zata yanke hukuncin ko zata tuhumi Villas-Boas ko kuma a'a.

Idan aka kamashi da laifi, za a iya dakatar dashi ko kuma aci tararsa.

Tuhumar da FA keyi nada nasaba akan yadda 'yan wasan Chelsea suka zagaye Foy lokacin da aka kori Bosingwa.