Fifa na binciken jami'an Caribbean su 10

fifa Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Tambarin FIFA a Zurich

Kwamitin da'a na Fifa ya soma bincike akan wasu karin jami'an kwallon yankin Caribbean su goma bisa zargin sayarda da kuri'a.

A ranar 14 ga watan Oktoba ne aka dakatar da wasu jami'an yankin su hudu.

Fifa a wata sanarwar ta ce jami'an zasu kare kansu ne a tsakiyar watan Nuwamba.

Ana tuhumarsu ce da saba ka'ida wajen hannu a cin hanci abinda ya janyo aka dakatar da Muhammed Bin Hammam daga kwallon kafa na tsawon rayuwa.

A watan Yuli, kwamitin da'a ya ce Bin Hammam ya nemi bada kyautar dala dubu arba'in ga duka jami'an kwallon yankin Caribbean su 25 a wani taro na musamman a Trinidad a watan Mayu.

Wannan batunne kuma ya janyo mataimakin shugaban Fifa Jack Warner yayi murabus.

Jami'an goma da Fifa ta bayyana sunayensu sune:Raymond Guishard (Anguilla), Damien Hughes (Anguilla), Everton Gonsalves (Antigua and Barbuda), Derrick Gordon (Antigua and Barbuda), Lionel Haven (Bahamas, CFU), Patrick John (Dominica), Philippe White (Dominica), Vincent Cassell (Montserrat), Tandica Hughes (Montserrat), Oliver Camps (Trinidad and Tobago).