Dole ne sai NFF ta biyani albashi na-Obuh

 John Obuh Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kocin Flying Eagles John Obuh

Tsohon kocin Najeriya a matakin 'yan kasada shekaru 17 da kuma 20 John Obuh ya ce dole ne sai hukumar kwallon kasar NFF ta biya shi bashin da yake binta.

A cewarsa yana bin NFF bashin albashin watanni 13 daga watan Disambar 2009 zuwa Disambar 2010.

Obuh ya jagoranci Najeriya zuwa zagayen gabda na kusada karshe a gasar cin kofin duniya ta 'yan kasada shekaru 20 a Columbia inda Faransa ta doke Flying Eagles.

Koda yake ana saran zai cigaba da mukaminsa a matakin 'yan kasada shekaru 20, amma Obuh ya ce hakurinsa na gushewa.

Obuh ya shaidawa BBC cewar"babu wani dalili da zasu biyani albashi daga watan Junairun 2011 zuwa Agustan 2011 amma suka ki biyan albashin shekara ta farko".

Ya kara da cewar"ina son aiki na amma kuma dole ne in dauki nauyin iyalai na, ina fatar NFF zata fahimta".

Kakakin NFF Ademola Olajire ya ce batun Obuh nada matukar takaici.

A kwanakin da suka wuce Christian Chukwu da Shaibu Amodu da Eucharia Uche da kuma Austin Eguavoen sun yi korafin cewar suna bin NFF kudin albashi.