Dan Barca Pedro zai yi jinyar makwanni uku

pedro Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Pedro Rodriguez

Dan kwallon Barcelona Pedro Rodriguez zai yi jinyar makwanni biyu zuwa uku saboda rauni a gwiwarsa.

Pedro ya jimu ne a wasan da Barca ta doke Granada daci daya me ban haushi a ranar Talata.

Sanarwar da Barca ta fitar ta ce "gwajin da aka gudanar akan Pedro ya nuna cewar yana fama rauni a gwiwarsa ta hagu". A don haka Pedro ba zai buga wasanni gasar La Liga guda biyu da kuma na zakarun Turai daya.

Sai dai Alexis Sanchez da Gerard Pique duk sun murmure kuma sun koma horo.