An sabunta: 27 ga Oktoba, 2011 - An wallafa a 09:07 GMT

Equatorial Guinea na gab da kimtsawa

Equatorial Guinea

Kwamitin shirya gasar ya ce saura kadan Equatorial Guinea ta kimtsa

An kusa kammala filayen wasan da za a taka leda a gasar cin kofin kasashen Afrika na 2012 a kasar Equatorial Guinea, a cewar kwamitin kula da shirya gasar.

Hukumar kula da kwallon kafa ta Afrika (Caf) na ziyar gani da ido kafin bikin raba kungiyoyin da za su taka leda a gasar da za a yi ranar Asabar a birnin Malabo.

Tawagar ta Caf ta kammala irin wannan ziyara a Gabon wacce za ta hada gwiwa da Equatorial Guinea wajen shirya gasar, kuma daga nan ne suka isa Malabo ranar Laraba.

"Kusan duka filayen wasan sun kammala," a cewar David Monsuy mai magana da yawun kwamitin.

"Akwai filin atisayi daya da ba a kammala ba a Malabo - amma an yi rabi a yanzu, haka kuma akwai daya a Bata - sai dai wajibi ne a kammala komai kafin watan Disamba.

"Ba zan iya magana a madadin Caf ba, amma dai na san mun yi iya kokarinmu wajen cika sharudan da suka shimfida mana na shirya gasar," kamar yadda Monsuy ya shaida wa BBC.

An gina wani sabon filin wasa a Bata, wacce za ta karbi bakuncin wasan farko na gasar a ranar 21 ga watan Janairu.

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.