Chelsea ta gamu da cikas na mallakar fili

Stamford Bridge Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Filin wasa na Stamford Bridge

Kokarin Chelsea na mallakar filin wasanta yaci karo da cikas a yayinda masu goyon bayan kulob din suka kada kuri'ar kin amincewa da cinikin.

Ana bukatar kashi saba'in da biyar cikin dari na masu hannun jarin mallakar filin wasa na Stamford Bridge su amince da cinikin amma kuma sai aka samu kashi 61 kadai suka amince.

A shekarar 1997 Chelsea ta cefanar da filin wasa na Stamford Bridge lokacin tana fuskantar matsalolin kudi.

A yanzu Chelsea na kokarin ta sayi filin wasan, sannan kuma ta canza mashi mazauni a yayinda galibin masu goyon bayan kulob din ke adawa da lamarin ganin cewar filin Stamford Bridge ya shafe fiye shekaru dari daya a inda yake a yanzu.

Sanarwar da kulob din ya fitar ta ce "Chelsea FC na cikin takaicin wannna sakamako abinda zai kawo tarnaki ga cigabanmu".

Ita dai Chelsea na ganin cewar filin Stamford Bridge mai daukar mutane dubu 42 na kawowa kulob din cikas wajen samun kudin shiga idan aka kwatanta da filin Arsenal maicin mutane dubu 60.