Inada kwarin gwiwa Van Persie zai zauna-Wenger

van Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Robin Van Persie

Kocin Arsenal Arsene Wenger ya ce yanada kwarin gwiwar cewa kyaftin dinsa Robin van Persie zai sanya hannu a sabuwar kwangila.

Van Persie ya zira kwallaye tara cikin wasanni 13 daya bugawa Arsenal a kakar wasa ta bana sannan kuma kwangilarsa zata kare ne a watan Yulin 2013.

Kawo yanzu dai Arsenal bata soma tattaunawa ba da Van Persie akan batun sabunta kwangilarsa, wanda shine kadai a tawagar yanzu daya lashe kofi tare da Arsenal.

Wenger ya shaidawa BBC cewar "yanada sauran watanni 18 kuma inada kwarin gwiwa zai sabuntata".

Arsenal ta zaku ta rike dan wasan mai shekaru 28 tun bayanda manyan 'yan wasanta Samir Nasri, Cesc Fabregas da Gael Clichy suka fice daga kulob din.

Amma dai Wenger ya siyo wasu 'yan wasan Yossi Benayoun da Mikel Arteta da Per Mertesacker da kuma Ju-Young Park a cikin tawagarsa.