CAN 2012:Ghana zata hadu da Mali

caf Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption A ranar 21 ga watan Junairu za a fara gasar

Kasashen da ake ganin sune zasu lashe gasar kwallon kasashen Afrika a 2012 wato Ghana da Ivory Coast sun gane abokan karawarsu a ranar Asabar.

Black Stars na Ghana na rukunin guda ne da Mali da Guinea da Bostwana kuma zasu kasance a birnin Frenchville na Gabon.

A yayinda ita kuma Ivory Coast zat fafata da Burkina Faso da Sudan da Angola kuma zasu kasance ne a birnin Malabo na Equitorial Guinea.

A ranar 21 ga watan Junairu ne za a buga wasan bude gasar tsakanin Equatorial Guinea da Libya a filin wasan na Bata.

Rukunin A: Equatorial Guinea, Libya, Senegal, Zambia (Bata)

Rukunin B: Ivory Coast, Sudan, Burkina Faso and Angola (Malabo)

Rukunin C: Gabon, Niger, Morocco and Tunisia (Libreville)

Rukunin D: Ghana, Botswana, Mali and Guinea (frenchville)