La Liga:Messi yaci kwallo uku,Real ta hau sama

mesiis Hakkin mallakar hoto AFP GETTY IMAGES
Image caption Lionel Messi

Lionel Messi na Barcelona yaci kwallaye uku cikin mituna goma sha takwas a wasan da Barca ta lallasa Mallorca daci biyar da nema a wasan da suka buga a filin Nou Camp.

Shi kuwa Gonzalo Higuain ya zira kwallo daya ne a wasan da Real Madrid ta samu galaba akan Real Sociedad daci daya me ban haushi a yayinda Real ta dare saman tebur.

Sakamakon wasu karawar mako na goma:

*Sporting Gijón 1 - 1 Athletic Club *Valencia 3 - 1 Getafe *Villarreal 2 - 0 Rayo Vallecano *Barcelona 5 - 0 Mallorca *Real Sociedad 0 - 1 Real Madrid