Serie A:Juventus da AC Milan sun haskaka

juverun
Image caption Alessandro Del Piero na Juventus

Juventus ta cigaba da jagorancin teburin gasar Serie A ta Italiya bayan ta bi Inter Milan har gida ta kuma doke ta daci biyu da daya.

Sai kuma AC Milan wacce ta har matakin na uku akan tebur sakamakon nasarar data samu akan AS Roma daci uku da biyu a wasan da suka buga a filin Stadio Olympico dake birnin Rome.

Sakamakon wasanni tara da aka buga, Juventus ta samu maki 19 sai Udinese ta biyu mai maki 18 a yayinda AC Milan keda maki 17.

Yadda ta kaya a sauran fafatawar:

*Catania 2 - 1 Napoli *Siena 4 - 1 Chievo *Bologna 3 - 1 Atalanta *Fiorentina 1 - 0 Genoa *Lecce 1 - 1 Novara *Parma 2 - 0 Cesena *Udinese 1 - 0 Palermo