2012:Namibia zata kai kara zuwa hukumar CAS

Namibia da Burkina Faso Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Namibia nada jaa akan Herve Zengue na Burkina Faso

Za a iya jefa gasar kwallon kafa na kasashen Afrika na 2012 cikin hargitsi bayan da Namibia tace zata kai kara wajen kotun kula da al'amuran wasanni wato CAS akan jin-in-jar dake tsakaninta da Burkina Faso.

A ranar Juma'a ne hukumar kwallon Afrika CAF ta kori karar da Namibia ta shigar gabanta akan tababa akan dacewar dan kwallon Burkina Faso Herve Zengue ya takama kasar leda.

A cewar hukumar kwallon Namibia zata daukaka kara a CAF sannan kuma idan ya kama zata kai kara wajen hukumar CAS.

Zengue wanda aka haifa a Kamaru amma matarsa 'yar Burkina Faso ce ya bugawa Burkina Faso wasannin share fage har guda biyu wadanda kasar ta doke Namibia.

Idan dan CAF ta kwace makin Burkina Faso ta baiwa Namibia tabbas da Namibia din ta tsallake zuwa gasar cin kofin kwallon kasashen Afrika.