Najeriya zata buga wasa a Benin da Kaduna

maigari Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Shugaban NFF Aminu Maigari

Super Eagles na Najeriya zata buga wasannin sada zumunci biyu a wata mai zuwa.

Kamar yadda shugaban hukumar kwallon Najeriya NFF Aminu Maigari ya bayyana, Najeriya zata kara da Botswana a ranar 12 ga watan Nuwamba a filin wasa na birnin Benin dake jihar Edo.

Sannan kuma a ranar 15 ga watan Nuwamba Najeriyar ta fafata da Zambia a filin wasa na garin Kaduna.

Maigari yace" Zamu kara da Botswana a Benin saboda mun samu kwarin gwiwa daga wajen gwamnan jihar Edo kuma zamu ji dadi saboda irin wasannin da tawagar 'yan kwallon Olympics dinmu suke bugawa".

A halin yanzu dai Najeriya bata koci sakamakon korar Samson Siasia a makon daya gabata.

Ana saran a ranar Laraba NFF zata sanarda nadin sabon koci.

Wasanni biyu zasu taimakawa Super Eagles a shirinta na neman gurbin zuwa gasar kwallon Afrika a 2013 sannan kuma ya baiwa sabon koci damar duba tawagar 'yan kwallon kasar.