An sabunta: 1 ga Nuwamba, 2011 - An wallafa a 13:09 GMT

Rooney da Messi da Ronaldo a jerin kyauta

messi

Messi ne gwarzon dan kwallon 2010

Wayne Rooney shine kadai dan Birtaniya dake cikin jerin mutane 23 wadanda za a baiwa mutum guda kyautar gwarzon dan kwallon duniya na bana wato Ballon d'Or .

Akwai 'yan Barcelona takwas cikin jerin hadda Lionel Messi wanda ya samu kyautar sau biyu a baya da Xavi Hernandez da Andres Iniesta da Dani Alves da Gerard Pique da David Villa da Eric Abidal da kuma Cesc Fabregas.

Akwai 'yan wasan Real Madrid biyar wato Cristiano Ronaldo da Iker Casillas da Xabi Alonso da Mesut Ozil da kuma Karim Benzema.

Akwai 'yan wasa uku dake taka leda a Ingila wadanda ke cikin jerin wato dan wasan Liverpool Luis Suarez dana Manchester United Nani sai kuma Sergio Aguero na Manchester City.

Dan Brazil Neymar shine kadai wanda ke taka leda a kudancin Amurka dake cikin jerin.

A ranar tara ga watan Junairu za a sanarda gwarzon a bukin da ayi a Zurich dake Switzerland.

Mutane 23 wadanda aka kebe:


Eric Abidal (Barcelona, France)
Sergio Aguero (Manchester City, Argentina)
Karim Benzema (Real Madrid, France)
Iker Casillas (Real Madrid, Spain)
Cristiano Ronaldo (Real Madrid, Portugal)
Daniel Alves (Barcelona, Brazil)
Samuel Eto'o (Anzhi Makhachkala, Cameroon)
Cesc Fabregas (Barcelona, Spain)
Diego Forlan (Inter Milan, Uruguay)
Andres Iniesta (Barcelona, Spain)
Lionel Messi (Barcelona, Argentina)
Thomas Mueller (Bayern Munich, Germany)
Nani (Manchester United, Portugal)
Neymar (Santos, Brazil)
Mesut Ozil (Real Madrid, Germany)
Gerard Pique (Barcelona, Spain)
Wayne Rooney (Manchester United, England)
Bastian Schweinsteiger (Bayern Munich, Germany)
Wesley Sneijder (Inter Milan, Netherlands)
Luis Suarez (Liverpool, Uruguay)
David Villa (Barcelona, Spain)
Xabi Alonso (Real Madrid, Spain)
Xavi (Barcelona, Spain)


Masu horadda 'yan wasa goma da aka kebe:

Vicente Del Bosque (ESP/Spain)

Sir Alex Ferguson (SCO/Manchester United)

Rudi Garcia (FRA/Lille)

Josep Guardiola (ESP/Barcelona)

Jurgen Klopp (GER/Borussia Dortmund)

Joachim Loew (GER/Germany)

Jose Mourinho (POR/Real Madrid)

Oscar Tabarez (URU/Uruguay)

Andre Villas-Boas (POR/Chelsea)

Arsene Wenger (FRA/Arsenal).

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.