Gerrard zai ji jinyar gwiwarsa ta dama

gerarrd
Image caption Steven Gerrard

Kyaftin din Liverpool Steven Gerrard ba zai buga wasan gasar Premier na ranar Asabar ba tsakaninsu da Swansea da kuma wasanni Ingila tsakaninta da Spain da kuma Sweden.

Dan wasan yana fama da ciwo ne a gwiwarsa ta dama.

Matsalar rauni ne a baya ya janyo Gerrard yayi jinyar watanni shida.

Ingila zata kara da Spain a Wembley a ranar 12 ga watan Nuwamba sannan bayan kwanaki uku ta fafata da Sweden.