FIFA ta yarda Ameobi da Moses su bugawa Najeriya

moses Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Victor Moses sanye da rigar Najeriya

Fifa ta amincewa tsaffin 'yan kwallon matasa a Ingila Shola Ameobi da Victor Moses su koma bugawa Najeriya kwallo.

Hukumar dake kula da kwallon Najeriya NFF ce ta nema Fifa ta bada wannan damar.

Kakakin NFF Ademola Olajire yace"Fifa ta yarda Ameobi da Moses su canza kasar da suke takawa leda".

Watakila a gayyaci 'yan kwallon biyu a wasan sada zumuncin da Najeriya zata buga da Botswana da kuma Zambia a wannan watan.

Ameobi da Moses duk sun bugawa Ingila kwallo a matakin 'yan kasada shekaru 21.

An haifi Ameobi a birnin Zaria kafin ya koma Ingila da iyayensa yana dan shekaru biyar.

Moses shi kuma an haifeshi a Kaduna amma ya koma Ingila yana shekara goma sha daya.