Newcastle ta lallasa Stoke da ci 3-1

Demba Ba Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wannan ne karo na biyu da ya zira kwallaye uku a kakar bana

Kwallaye ukun da Demba Ba ya zira sun taimaka wa Newcastle ta doke Stoke City da ci 3-1, inda ta koma mataki na uku a teburin gasar Premier ta Ingila.

Dan wasan na Senegal ya fara zira kwallon farko ne a minti na 12, sannan ya kara zira ta biyu kafin a tafi hutun rabin lokaci.

Sai dai Ba ya so ya dakushe rawar da ya taka bayan da ya ture Peter Crouch na Stoke abinda ya baiwa Stoke din damar samun bugun fanareti ana saura minti 15 a tashi.

Sai dai ba tare da wani bata lokaci ba, sai Ba ya zira kwallo ta uku daga bugun fanareti bayan da aka tade Leon Best.

Wannan ne karo na biyu da ya zira kwallaye uku a kakar bana, kuma a yanzu ya zira kwallaye takwas kenan.

Yayin da su kuma tawagar ta Alan Pardew suka hau saman Chelsea a mataki na uku da maki 22.

Wannan ne kuma karo na farko da Stoke ta sha kashi a filin wasa na Britannia Stadium a kakar wasa ta bana.