Toure na jiran makomarsa a Manchester City

toure
Image caption Toure da Mancini

Manchester City ta kamalla bincike akan Kolo Toure saboda batun shan haramtacciyar kwaya, kuma a ranar bakwai ga wata za a bada sakamako.

An dakatar da Toure na watanni shida bayan da aka gwada jininsa aka gano cewar ya sha haramtacciyar kwaya me kara kuzari.

Dan wasan mai shekaru 30 ya buga wasanni hudu tunda ya dawo buga kwallo a watan Satumba, kuma watakila aci tararsa albashin makwanni shida ko kuma kulob din ya dakatar dashi.

Shugaban kungiyar 'yan kwallo a Ingila Gordon Taylor ya ce Toure ya girgiza a zaman kwamitin da'a na kulob din.

Kocin Manchester City Roberto Mancini ya ce duk da wannan batun, Toure ba zai daina bugawa kulob din leda ba.