Za'a yi wa Harry Redknapp tiyata

Harry Redknapp
Image caption Harry Redknapp yana haskakawa sosai a Spurs

Tottenham ta tabbatar da cewa koci Harry Redknapp zai gana da likitoci kan wata rashin lafiyar da yake fama da ita wacce basu bayyana ba kawo yanzu.

Kocin mai shekaru 64 ba zai halarci wasan da za su kara da Rubin Kazan a gasar cin kofin Europa League a Rasha ranar Alhamis ba.

Spurs ce ta daya a rukunin na A, inda ta baiwa PAOK na Girka tazarar maki biyu.

Mataimakin koci Kevin Bond da kuma kocin tawagar farko na kulob din Joe Jordan ne za su jagoranci Tottenham a madadin Redknapp.