Siasia ya gurfanar da NFF gaban kuliya

siasia Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Samson Siasia

Tsohon kocin Super Eagles Samson Siasia ya gabatar da hukumar kwallon Najeriya NFF kara a gaban kotu saboda kararsa da aka yi a ranar Juma'ar data gabata.

Siasia ya kai karar NFF ne akan batun saba ka'idar kwangila bayanda aka koreshi saboda ya kasa tsallakar da kasar zuwa gasar cin kofin Afrika a 2012.

A cewar NFF ta kori Siasia ne saboda bai cimma sharudan da aka gidayamasa ba a lokacin da aka nada shi kocin Super Eagles.

Sai dai Siasia na cewar NFF ta saba ka'ida wajen korarsa saboda kwangilar da suka sanyawa hannu tace sai a bashi sanarwa kwanaki talatin kafin a koreshi.