'Yan wasan kurket uku za su jarum

Salman Butt Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Kotu ta yankewa wasu 'yan wasan Kurket din kasar Pakistan su uku hukuncin daurin gidan yari ciki har da tsohon keftin din wasan Kurket din Salman Butt

An yankewa wasu 'yan wasan Kirket ukku 'yan kasar Pakistan hukuncin dauri a gidan yari, bayan da aka same su da laifi akan hada baki wajen yin jinga a wasan.

An yankewa tsohin kyaftin din yan Kirket na Pakistan din, Salman Butt hukuncin daurin shekaru biyu da rabi, yayin da aka yankewa Mohamemd Asif, wanda shine tsohon fitaccen dan wasa na biyu a duniya, daurin shekara daya.

Sai kuma wani dan wasan mai suna Mohd Amir, wanda ya amsa laifinsa, inda aka yanke masa hukuncin daurin watanni shidda a gidan kaso.

Tsohon keptin din kwallon kirket din kasar Ingila Michel Vaughan yace kamata ya yi ace a dakatar dasu daga buga wasan har tsawon rayuwarsu

'Yace ina fata wannan hukunci zai sa 'yan wasan kurket su shiga taitayinsu nayi farinciki game da yadda aka tunkari lamarin, kuma yace yayi imanin cewar har yanzu akwai abinda ya kamata ayi domin a hukunta masu irin wannan laifi fiye da wadanda ake dasu yanzu