Victor Moses zai takawa Super Eagles wasa

'Yan wasan Najeriya na Super Eagles
Image caption Wasan da Najeriya zata taka da kasashen Bostwana da Zambia shine wasa na farko da sabon mai horar da 'yan wasan Najeriya Stephen Keshi zai jagoranta

Najeriya ta sanya sunan Victor Moses a cikin tim din 'yan wasan da zasu buga wasan sada zumunta da kasashen Botswana da Zambia a cikin wannan watan

An dai gayyaci dan wasan dan shekaru 20 mai buga wa kungiyar kwallon kafa ta Wigan wasa a karo na farko domin ya buga wasan Kofin Afirka da Najeriya ta buga da Kasar Ethiopia a cikin watan Maris din daya gabata, amma sai dai dan wasan bai sami damar taka wasan ba saboda hukumar kwallon kafa ta duniya wato FIFA bata wanke ba domin ya bugawa kasar ta sa ta haihuwa wasa.

Hukumar kwallon kafa ta Najeriya dai wato NFF ta fitar da sunayen 'yan wasa su 28 da zasu taka wasan sada zumuntar da kasashen Zambia da Bostwana a nan gaba

Kuma wannan shine wasan farko da sabon mai horar da 'yan wasan Najeriya Stephen Keshi zai jagoranta

Masu tsaron gida sun hada da: Vincent Enyeama (Lille, France), Austin Ejide (Hapoel Petah Tikva, Israel), Chigozie Agbim (Warri Wolves)

'Yan baya: Chibuzor Okonkwo (Heartland), Gege Soriola (Free State Stars, South Africa), Taye Taiwo (AC Milan, Italy), Elderson Echiejile (Sporting Braga, Portugal), Joseph Yobo (Fenerbahce, Turkey), Efe Ambrose (Ashdod MS, Israel), Ayodele Adeleye (SC Tavriya Simferopol, Ukraine), Ugo Ukah (Widzew Lopdz, Poland), Yusuf Ayila (Dynamo Kiev, Ukraine)

'Yan wasan tsakiya sun hada da: John Mikel Obi (Chelsea, England), Fengor Ogude (Valerenga, Norway), Kalu Uche (Neuchatel Xamax, Switzerland), Nosa Igiebor (Hapoel Tel Aviv, Israel), Dickson Etuhu (Fulham, England), Victor Moses (Wigan Athletic, England), Joel Obi (Inter Milan, Italy)

'Yan wasan gaba sun hada da: Obinna Nsofor (Lokomotiv Moscow, Russia), Ahmed Musa (VVV Venlo, Netherlands), Ikechukwu Uche (Granada, Spain), Osaze Odemwingie (West Bromwich Albion, England), Ekigho Ehiosun (Samsunspor, Turkey), Emmanuel Emenike (Spartak Moscow, Russia), Chinedu Obasi (TSG Hoffenheim, Germany), Brown Ideye (Dynamo Kyiv, Ukraine), Edward Ofere (US Lecce, Italy)