Boateng ya daina bugawa Ghana kwallo

Kevin-Prince Boateng Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption A bara ne Kevin-Prince Boateng ya fara takwa Ghana leda

Dan wasan Ghana da AC Milan Kevin-Prince Boateng ya ce ya daina takawa kasar Ghanan leda saboda abubuwa sun yi masa yawa.

Hukumar kula da kwallon kafa ta kasar Ghana ta tabbatar da hakan a wata sanarwa da ta fitar a shafinta na intanet. A wasikar da dan wasan mai shekaru 24 ya aike wa hukumar, ya bayyana "wahala wajen bugawa kulob da kuma kasa" cewa shi ne dalilinsa na daukar matakin.

Boateng ya fara taka wa Ghana leda ne bara bayan ya wakilci Jamus a matakin 'yan kasa da shekaru 21 da kuma na matasa.

Hukumar kula da kwallon kafa ta duniya FIFA, ta bashi damar buga wa Ghana kwallo a gasar cin kofin duniya da aka yi a Afrika ta Kudu bara, inda kasar ta kai matakin wasan dab dana kusa dana karshe.

Boateng ya taka wa Ghana leda sau tara, inda ya zira kwallo daya.