An sanya Terry a tawagar Ingila

John Terry Hakkin mallakar hoto PA
Image caption John Terry ya musanta zargin da ake yi masa

BBC Ta fahimci cewa an saka kyaftin John Terry a jerin 'yan wasan Ingila da ake sa ran za su fafata a wasan sada zumunta da Spain da kuma Sweden.

Sai dai koci Fabio Capello zai tattaunawa da manyan jami'an hukumar kula da kwallon kafa ta Ingila FA, kafin ya yanke shawarar ko zai sanya Terry a jerin sunayen karshe na 'yan wasan da za su taka leda a wasannin biyu.

Ana bincike kan kyaftin din na Chelsea bayan da aka zarge shi da yin kalaman wariyar launin fata ga Anton Ferdinand na QPR.

An fahimci cewa Terry na son ya taka leda a wasannin da Ingilan za ta kara.

An sanar da 'yan wasan da aka gayyata ranar Alhamis kuma za a bayyana jerin sunayen na karshe ranar Lahadi da dare.

Capello zai gana da shugaban FA David Bernstein, Sakatare Janar Alex Horne da Adrian Bevington, Manajan da ke kula da kungiyoyi a Ingila, kafin ya yanke shawara kan Terry.