Watakila Adebayor ya koma bugawa Togo kwallo

adeyar
Image caption Emmanuel Adebayor

Emmanuel Adebayor na tattaunawa da hukumar kwallon Togo akan batun sake komawa cikin tawagar 'yan kwallon kasar.

Dan wasan mai shekaru 27 watakila ya koma takawa tawagar Hawks leda a wasanta da Guinea Bissau na share fagen buga gasar kwallon duniya a 2014.

Yanzu shekara biyu kenan rabon da dan kwallon Tottenham din ya bugawa kasarsa kwallo.

Adebayor ya shaidawa BBC cewar "Zan tattauna da hukumar kwallon Togo kuma watakila mu cimma yarjejeniya".

Adebayor ya yo ritaya daga kwallon Togo a shekara ta 2010 bayan da aka kaiwa tawagar kwallon kasar hari a Angola inda mutane biyu suka rasu.