Tennis: Andy Murray ya doke Chardy

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Andy Murray

Dan wasan Tennis din Burtaniya, Andy Murray ya tsallake zuwa zagaye na biyu a gasar Tennis din Paris Master bayan ya doke dan Faransa, Jeremy Chardy.

Murray ya doke Chardy ne a wasanni biyu da maki 6-2 6-4.

Nassarar da Murray ya samu ya zama 17 a jere da ya yi a fagen Tennis.

A yanzu haka dai zai kara ne da Andy Roddick domin shiga gurbin wasan gab da kusa dana karshe.