An ci tarar Kolo Toure a Manchester City

toure Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kolo Toure

An ci tarar dan kwallon bayan Manchester City Kolo Toure albashinsa na makwanni shida saboda shan haramtaciyyar kwaya mai kara kuzari.

A watan Mayu ne aka dakatar da Toure na watanni shida bayan da aka gwada jininsa aka gano ya sha kwaya.

Dan kasar Ivory Coast din mai shekaru 30 ya buga wasanni biyar ne kacal tun bayan da ya dawo taka leda a watan Satumba.

Sanarwar da City ta fitar ta ce"Kolo ya amince da hukuncin kuma shi da kulob din zasu tattauna akan yadda za a fuskanci gaba".

Shugaban kungiyar kwararrun 'yan kwallon PFA Gordon Taylor ya bayyanawa kwamitin da'ar Manchester City cewar sun girgiza da aka gano cewar Toure ya sha kwaya.

Shi kuwa kocin City Roberto Mancini ya ce za a cigaba da baiwa Toure dama ya buga kwallo a kulob din.