Adebayor zai koma bugawa Togo kwallo

Emmanuel Adebayor Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Emmanuel Adebayor

Emmanuel Adebayor zai koma bugawa Togo kwallo bayanda hukumar kwallon kasar ta tabbatar masa cewar zata kare lafiyarsa.

Dan wasan a baya yayi ritaya daga bugawa Togo kwallo sakamakon harin da aka kaiwa tawagar 'yan kwallon kasar inda mutane biyu suka mutu a Angola a shekara ta 2010.

Adebayor mai shekaru 27 ya tattauna da hukumar kwallon kasar kafin ya yanke hukunci a ranar Laraba.

A don haka dan kwallon Tottenham din zai bugawa Togo kwallo a wasanta da Guinea Bissau a mako mai zuwa na neman gurbin zuwa gasar kofin duniya a 2014.

Adebayor yace"Nayi farin cikin komawa Togo kuma zan buga mata kwallo a mako mai zuwa tsakaninta da Guinea Bissau".

Adebayor a halin yanzu yana matsayin aro a Tottenham Hotspurs daga Manchester City.

Karin bayani