Siasia ya janye karar daya kai NFF a Kotu

siasia Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Samson Siasia

Tsohon kocin Najeriya Samson Siasia ya janye karar da ya shigar gaban kotu akan korarsa da hukumar kwallon Najeriya NFF tayi a watan daya gabata.

A don haka kuma Siasia ya ce yana goyon bayan Stephen Keshi don samun nasara a matsayin kocin Super Eagles.

NFF ta kori Siasia ne bayanda ya kasa tsallakar da kasar zuwa gasar cin kofin kwallon kasashen Afrika da za ayi a badi.

Amma gabda fara sauraron karar a gaban kotu, Siasia ya canza shawara inda yace zai fuskanci gaba.

Siasia ya shaidawa BBC cewar "na yanke shawarar janye karar dana kai NFF kuma maganar ta mutu kenan".

A baya Siasia ya kasance wanda ake matukar so a Najeriya bayanda ya jagoranci tawagar 'yan kasada shekaru 20 takai wasan karshe a gasar kofin duniya sannan kuma ya jagoranci 'yan kasada shekaru 23 suka lashe kyautar azurfa a gasar Olympics a Beijing a shekara ta 2008.

Karin bayani