Hukumar FA ta tuhumi Villas-Boas

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kocin Chelsea, Andre Villas Boas

Hukumar kwallon Ingila wato FA ta tuhumi kocin Chelsea, Andre Villas-Boas da rashin da'a bayan kalaman da ya yi a kan alkalin wasa Chris Foy.

Kocin dai ya yi hakan ne, bayan kashin da kungiyarsa ta sha a hannun QPR da ci daya mai ban haushi.

Kocin ya amince cewa ya nunawa alkalin rashin mutunci, bayan da ya sallami Jose Bosingwa da Didier Drogba, sannan kuma aka nunawa 'yan wasan Chelsea katin gargadi bakwai.

"Mun tuhumi, Villas-Boas da rashin da'a," In ji wata sanarwa da Hukumar FA ta fitar.

Sanarwar ta kara da cewa; "Yana da har zuwa karfe hudu na GMT a ranar 15 na watan Nuwamba, domin ya mayarda martani."