Lampard zai jagoranci Ingila a wasa da Spain

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Frank Lampard na murnar zura kwallo a kungiyarsa ta Chelsea

Fabio Capello ya nada Frank Lampard a matsayin kyaftin Ingila a wasan sada zumuncin da kasar za ta buga da Spain a ranar Asabar.

Har wau ya John Terry ne zai ci gaba da rike mukaminsa a wasan da kasar za ta buga da Sweden.

Amma kocin Ingilan ya ce zai ci gaba da aiki da Terry, har sai an same shi da laifi.

Jami'an 'yan sanda dai na binciken Terry ne bayan da ake zargin shi da yiwa dan wasan QPR, Anton Ferdinand, kalamun wariyar launin fata.

"Na dau matakin baiwa Lampard kyaftin ne kafin a fara zargin Terry." In ji Capello.

"Terry zai zauna ne a benci a wasa da Spain amma zai buga a wasanmu da Sweden." In ji Capello.

Capello ya nace cewa Terry na da goyon bayansa da kuma na Hukumar kwallon Ingila.