Dolhins ta Fatakwal ta lashe gasar Najeriya

npl
Image caption Tambarin gasar premiet ta Najeriya

Kungiyar Dolphins ta garin Fatakwal ta lashe gasar premier ta Najeriya a bana sakamakon nasarar data yi akan Bukola Babes daci daya me ban haushi a wasan da suka buga a birnin Ilori. Sunshine Stars ta Akure ce ta kasance ta biyu a gasar bayan ta sha kashi a wajen Kano Pillars daci daya me ban haushi. A yayinda Warri Wolves ta jihar Delta ta tashi kunen doki tsakaninta da Niger Tornadoes a garin Minna.

Sakamakon wassannin karshe:

*Niger Tornadoes 1- 1 Warri Wolves *Sharks 1 - 0 Kwara United *Rangers International 1- 0 Crown FC *Plateau United 1- 0 Heartland FC *Shooting Stars 1 - 0 Lobi Stars *Bukola Babes Dolphins FC *Zamfara United 1- 1 Ocean Boys *Kano Pillars 1- 0 Sunshine Stars *Gombe United 2- 0 Kaduna United *Enyimba 2 - 0 JUTH FC