Zan sadaukar da kai a Togo-Adebayor

adebayor Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Emmanuel Adebayor

Dan kwallon Togo Emmanuel Adebayor ya sha alwashin takawa kasar leda iyaka kokarinsa idan ya koma fagen fama a ranar Talata bayan shafe kusan shekaru biyu baya bugawa kasarsa kwallo.

Dan shekaru 27 zai buga wasansu da Guinea Bissau a birnin Lome a wasan neman gurbin zuwa gasar cin kofin duniya da za ayi a shekara ta 2014.

Hakan dai ya biyo bayan shawarar dan wasan Tottenham din ya janye ritayar da yayi a makon daya gabata.

Magoya bayan kasar da dama ne suka yi tururuwa don kallon dawowar dan wasan Togon.

Adebayor yace"kamar yadda kuka gani magoya baya dama ne suka zo bakin kan iyaka don taya ni murna,to idan ban buga wasanmu na ranar Talata ba nayi abin kunya".

Tun bayan da Adebayor ya daina bugawa Togo kwallo kasar ta fuskanci matsaloli inda takasa tsallakewa zuwa gasar cin kofin Afrika da za ayi a 2012.