Dan wasan Najeriya Elejiko ya mutu a Belgium

Bobsam Elejiko Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Margayi Bobsam Elejiko

Dan kwallon Najeriya Bobsam Elejiko ya mutu a daidai lokacin da yake bugawa kulob dinsa a Belgium Merksem SC a ranar Lahadi.

Dan wasan bayan mai shekaru ya suma ne a wasansu da FC Kaart daga nan sai yace ga garinku.

An yita kokarin ceto ransa amma abin ya faskara.

Merksem a wata sanarwar data fitar ta ce"cikin juyayi,muna sanar da mutuwar Bobsam Elejiko".

Sakamakon mutuwar Elejiko dai, an dakatar da wasan.

Tarihin kwallon Bobsam Elejiko: * Wacker Nordhausen, Germany (2000-01) * Turnhout, Belgium (2001-03) * Westerlo, Belgium (2003-07) * Royal Antwerp, Belgium (2007-08) * SC Beira-Mar, Portugal (2008) * Deinze, Belgium (2009) * Red Star Waasland, Belgium (2009-10) * Merksem, Belgium (2011)