'Yan Kamaru sun ki buga kwallo saboda kudi

Indomitable Lions Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Indomitable Lions

'Yan kwallon Kamaru sun ki tafiya don buga wasan sada zumunci saboda takaddama akan kudi.

Ya kamata su buga wasa tsakaninsu da Aljeriya a ranar Talata amma kuma sai aka fasa buga wasan.

Takaddamar ta kunno kai ne bayanda 'yan wasan Indomitable Lions suka buga wasanni biyu tsakaninsu da Morocco da kuma Sudan.

Ganin cewar ba a biyasu kudaden alawus dinsu dana garabasa ba, sai suka ce ba zasu buga wasan da Aljeriya ba.

'Yan wasan a wata sanarwa sun ce "matsala akan kudin alawus a makon daya gabata har yanzu ba a warware ba".

Suka kara da cewar "'Yan wasan babbar tawagar na kishin kasa kuma suna kira ga shugabannin kwallo a Kamaru su cika alkawari".

Wannan takaddamar babbar matsala ce ga sabon kocin Kamaru Denis Lavagne wanda ya maye gurbin Javier Clemente wanda aka kora a watan daya wuce.