Najeriya ta doke Zambia daci biyu da nema

najeriya
Image caption Super Eagles

Tawagar Super Eagles ta Najeriya ta doke Chipolopolo ta kasar Zambia daci biyu da nema a wasan sada zumuncin da suka buga a filin wasa na Ahmadu Bello dake Kaduna.

Kalu Uche ne ya fara ciwa Najeriya kwallon farko sannan Ike Uche yaci na biyu ana sauran 'yan mintuna a tashi wasan.

Wannan ne wasa na biyu da Stephen Keshi ya jagoranci Najeriya tun bayan da aka kori Samson Siasia a watan daya gabata.

Najeriya dai ta barar da kwallaye da dama a wasan, a yayinda ita kuma Zambia ta gamu da rashin sa'a da ta ci kwallaye akalla biyu itama.